Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Na Shan Suka kan Kungiyar IPOB


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki.

Yayinda shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ke neman mafita daga kalamun da yayi na cewa ayana kungiyar IPOB a matasayin ta 'yan ta'adda da gwamnatin Buhari ta yi baya kan ka'ida, wasu 'yan majalisar cewa suka yi karya ya keyi kuma burin son zama shugaban kasa ya sashi yin kalamun.

A na cigaba da muhawara kan matsayar shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki wanda ya nuna ayyana kungiyar 'yan awaren Biafra da rundunar sojojin Najeriya ta yi ya sabawa doka.

Bukola Sarakin wanda ya ce ba'a bi ka'ida ba wajen daukan matakin bayyana kungiyar a matsayin ta 'yan ta'adda ya kawo cecekuce da rabuwan kawuna a kasar. Kalamun nasa sun jawo suka mai tsanani daga wasu 'yan Najeriya da suka dauki kungiyar IPOB da Nnamdi Kamu ke jagoranta a matsayin kungiya nai mummunar akida.

Shugaban kwamitin labaru na Majalisar Sanata Aliyu Sahabi yace ba'a fahimci Bukola Sarakin ba ne. "Amma duk da haka ya nemi ahuwar jama'a", inji Sanata Sahabi. Yana mai cewa kada a dauki furucin Bukola Saraki tamkar Majalisar tana adawa ne da gwamnatin tarayya.

Amma dan majalisar wakilai Babba Kaita ya tsame majalisarsu daga kalamun Bukola Saraki. Ya kara da cewa "karya yake bai isa ba. Na biyu ina jin Saraki ya makance ne. Babu abun da yake tunane sai maganar yaya za'a yi yayi mulkin Najeriya. Shi ya sa zai ga 'yan ta'adda masu zub da jini yace ba haka ba ne. Ta'addanci daya ne. Ko a yishi a Ilorin ko Katsina ko Enugu. Ta'addanci iri daya ne. Military suna da hurumi su ce wannan kungiya ta 'yan ta'adda ce. Kuma tayi haka, kuma ta zauna. Wannan aiki ne na bangaren zartaswa"

Kaita ya kara da cewa kila abun da Saraki ke cewa shi ne a kai kungiyar gaban alkali a kotu a kasheta kuma gwamnati ta yi hakan. Injishi, duk mai tunane da kuma mai kishin Najeriya zai tabbatar cewa wannan abun an yishi bisa ga ka'ida kuma an yishi don a samu zaman lafiya.

Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan Shari'a Abubakar Malami ta ce bakin alkalami ya bushe kan matakin. Acewarsa akwai doka ta ta'addanci da ta baiwa shugaban kasa ikon haramta duk wata kungiya dake ta da hankali da hana zaman lafiya.

Ga rahoton Saleh Ashaka da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG