Tsohon shugaban majalisar ya rubuta wasikar sauka daga mukaminsa saboda zargin karbar cin hanci daga Alhaji Aliko Dangote akan binciken da majalisar ta ke yiwa sarkin Kano.
Tuni 'yan majalisar suka amince da wasikar tsohon kakakin na yin murabus suka kuma maye gurbinsa da Onarebul Abdullahi Ata a matsayin sabon shugaba.
Sabon shugaban ya yi alkawarin tafiya da kowa domin a kawo cigaba. Ya bukaci addu'a da goyon baya.
Bayan ta samu sabon shugaba majalisar ta kafa kwamitin bincike akan tsohon shugaban majalisar akan batun karbar Naira miliyan dari daga Aliko Dangote.
To saidai Onarebul Bappa Dan Agundi dake goyon bayan tsohon kakakin majalisar yace kamata ya yi majalisa ta mikawa hukumar EFCC binciken maganar domin majalisar da shugabanninta aka zarga da karbar kudin.
Amma tsohon shugaban yace zai baiwa kwamitin binciken hadinkai.
A saurari karin bayani daga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum