Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Nemi a Sanya Wa Belarus Takunkumi


Shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai Charles Michel, ya yi kira da a duba yiwuwar gaggauta sanya takunkumi akan hukumomin Belarus, bayan kulle shugabannin 'yan adawa da yawa da suka yi.

“Muzgunawar siyasa a Belarus ciki har da kulle jama’a bisa dalilan siyasa da kuma talisata barin kasar, dole ne a dakatar da su, abinda Michel ya rubuta kenan a shafinsa na Twitter a jiya Laraba. Ya kara da cewa Dole ne hukumomin Belarus su saki fursunonin siyasa su kuma bai wa ‘yan kasar damar ‘yancinsu na fadin albarkacin baki, da kuma yin taro.

Wasu jami’an gwamnatin kasar da ba a sani ba, a jiya Laraba suka kama sauran shugabannin ‘yan adawar kasar 2, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna kin jinin dadadden Shugaba Alexander Lukashenko, biyo bayan zaben kasar da ya bar baya da kura.

Wasu mutane da ba a sani ba, da suka rufe fuskokinsu sun je ofishin 'yan adawar suka fidda Attorney Maxim Znak, a cewar Gleb Geman wani na kusa da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG