Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Mali Zai Gabatar da Bukatun Kasashen Sahel Renon Faransa a Taron MDD


Shugaban Mali Ibrahim Bubakar Kaita yana ta hannun hagu da shugaban Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban Mali Ibrahim Bubakar Kaita yana ta hannun hagu da shugaban Nijar Issoufou Mahamadou

A yunkurin da suka sa gaba domin samun kasashen duniya su taimaka da kudaden gudanar da rundunar tsaron kasashen Sahel renon Faransa da suka hada da Chadi, Burkina Faso,Mauritania,Mali da Nijar sun dorawa shugaban kasar Mali nauyin gabatar da bukatunsa a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Akan wannan ne Ibrahim Bubakar Keita ya ziyarci kasar Nijar a cigaba da zagayawa kasashen Sahel din domin tattara shawarwarin da zasu gamsar da masu hannun da shuni, injishi.

Shi ma shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou mai masaukin baki ya kara da cewa abun da kasashen suka sa gabansu magana ce da ta shafi duniya gaba daya kuma muddin 'yan ta'adda suka samu nasarar ruguza matakin da kasashen ke dauka matsalar ka iya kutsawa zuwa kasashen yammacin turai.

A cewar shugaban Nijar nauyi ya rataya a wuyan kasashen duniya su tabbatar sun bada gudummawa domin ganin an dakile matsalar tun kafin ta bunkasa.

Kimanin dalar Amurka dari hudu da sihirin da biyar ne ake bukata domin gudanar da ayyukan dakarun da kasashen suka kafa domin yakin ta'addanci. Kowace kasa dake cikin hadin gwuiwar ta yi alkawarin bada dalar Amurka miliyan goma sha biyu. Tarayyar Turai ta bada miliyan hamsin na Euro. Kasar Faransa ta yi alkawarin tallafawa da miliyan takwas na Euro.

Saboda haka ne ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakuba yace neman taimakon kasashen waje ya zama tilas. Ministan na ganin akwai alamar haske a taron na New Yorka da za'a yi makon gobe. Dakarun kasashen nada sojoji dubu biyar ne.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG