Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Masar Hosni Mubarak

Tsohon Shugaban Masar mai fuskantar shari'a Hosni Mubarak

Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak ya sake gurfana a gaban wata kotu a birnin al-Khahira don sake fuskantar shari’a game zargin hannu a mace-macen daruruwan masu zanga-zanga a yayin boren zaburowar Larabawa na 2011.

Shari’ar ta yau Asabar maimaici ne. An zartas ma Mubarak hukuncin daurin rai da rai bara game da wannan tuhumar, to amma sai aka yadda a sake yin shari’ar bayan daukaka karar da masu karar da masu kare shi su ka yi saboda wani kuskuren tsari da aka yi.

Mubarak ya bayyana gaban kotun a yau Asabar ne bisa kujera mai tayu. ‘Ya’yansa biyu na ganga da shi, wadanda su ma ake zarginsu kan wasu batutuwa na dabam na cin hanci da rashawa.

An dau tsauraran matakan tsaro a wajen kotun, inda ‘yan uwan wasu da abin ya rutsa da su su ka taru.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG