Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai jagoranci kwamitin kula da rmata da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya


Mata da yaron ta suna fama a asibiti

Ban ki Moon ya zabi shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin daya daga cikin yan kwamitin kula da ceto rayukan mata da yara

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban ki Moon ya zabi shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin daya daga cikin shugabannin kwamitin da kula da ceto rayukan mata da kanananan yara.

Shugaban Najeriyan zai shugabanci kwamitinshi tare da firai Ministan kasar Norway Jean Stoltenberg, a shirin gangamin Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya da ake kira “kowacce Mace, Kowanne yaro” ko kuma “Every Woman Every Child” a turanci da nufin cimma muradun karni.

Da yake kaddamar da kwamitin, Mr. Ban yace, tabbatar da cewa, mata da kananan yara suna samun magunguna da sauran muhimman abubuwan da suke bukata yana da muhimmanci a yunkurin cimma muradun karni.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar zata sa ido kan muhimman tsare tsaren lafiya domin tabbatar da kare lafiyar mata da kananan yara daga kamuwa da cutukan dake haddasa kisa ko kuma kwantar da su.

Hukumar zata kuma kunshi cibiyoyin da abin ya shafa, kama daga daidaikun mutane da kungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatan gwamnati.

Darektar asusun tallafawa kanannan yara UNICEF Anthony lake da darektan UNFPA Dr. Babatunde Osetimehin zasu yi aiki a matsayin mataimakan shugabannin kwamitin,

A cikin jawabinshi, shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, kula da lafiyar mata da kanannan yara yana daya daga cikin muhimman ayyukan da kasar ta sa gaba.

Bisa ga cewarshi, za a iya ceton rayuka ta wajen samar da magunguna isassu da kayan aikin jinya. Ya kuma ce “tilas ne nu tashi tsaye mu taka rawar gani yanzu.”

XS
SM
MD
LG