Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya isa New York domin halartar taron koli na Majalisar Dinkin Duniya, mdd, na wannan shekarar ta 2017.
Shugaban zai yiwa zauren taron jawabi akan matsalolin yaki da cin hanci da rashawa da yaki da ta'addanci da kuma bukatar dake akwai.
Shugaban zai nemi kasashen duniya gaba daya su baiwa Najeriya goyon bayan da take bukata domin ta bunkasa tattalin arzikinta.
Malam Garba Shehu kakakin fadar shugaban Najeriya ya yi karin haske akan ziyarar. Yana mai cewa baicin jawabin da shugaban zai yi a zauren taron kolin akwai wasu tarurruka da kuma zai yi.
Bayan an bude taron yau shugaban zai halarci taron kare mutuncin mata wadanda sau tare ake yi masu fyade da sacesu tare da nuna masu fin karfi a duk fadin duniya.
Yana da zama na musamman dashi da shugaban Amurka Donald Trump. Zasu ci abincin rana tare kana su tattauna kan wasu abubuwa.
Dangane da ko 'yan rajin kafa kasar Biafra zasu yi masa zanga zanga, Malam Shehu yace babu hakan saboda matakan da kasar ta dauka.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum