Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Umarci Gwamnoni Su Biya Ma’aikata Albashi kafin Bikin Kirisimeti


Shugaba Buhari Tare Da Gwamnonim Jahohin Najeriya
Shugaba Buhari Tare Da Gwamnonim Jahohin Najeriya

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya gana da gwamnonin jihohin kasar a fadarsa dake Abuja, inda batun basussukan albashin ma’aikata ya mamaye taron.

A lokacin taron shugaba Buhari ya ja kunnen gwamnonin jihohin kasar da su gaggauta biyan basussukan albashi ga ma’aiakata kafin bikin Krismeti na watan gobe.

Shugaban wanda ya bayar da umarnin biyan kashi 50 daga cikin dari na karshe ga jihohi daga kudaden da aka dawo da su na Paris Club, ya nuna muhimmancin biyan albashi.

Da yake yiwa manema labarai karin bayani, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yace batun ma’aikata ne ya mamaye taron da suka yi da shugaba Buhari, inda shugaban ya nuna damuwarsa musamman kan ma’aikatan da suka dogara kan albashi domin su ciyar da iyalansu da biyan kudin haya.

Gwamnonin dai sun tabbatarwa shugaban cewa da zarar sun sami kudaden Paris Club, to kowacce jiha zata dage ta biya ma’aikatanta albashi.

Sai dai gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Ahmad El-Rufa’I, ya ce ma’aikatan jihar basa bin gwamnati bashin albashi, amma yace wasu jihohin bashin da ake binsu yafi kudaden Paris Club din da zasu samu a yanzu.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG