Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Yaba da Rawar da Red Cross Ta Taka Wajen Sako 'Yan Chibok


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yaba da irin muhimmiyar rawar da kasashen kasa da kasa irin kungiyar bada agaji ta Red Cross da wasu kasashe suka taka wajen sako wasu 'yan matan Chibok 21 cikin wadanda aka sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Yayinda yake ganawa da Mr. Peter Maurer shugaban kungiyar Red Cross a fadarsa dake Abuja yau Litinin, shugaba Muhammad Buhari yace gwamnatinsa ashirye take ta cigaba da tattaunawa da kungiyar Boko Haram "muddin ta yarda da shiga tsakanin kungiyoyi irinsu Red Cross.

Yace "Munga sakamakon tattaunawar da muka yi kwana kwanan nan gashi 'yan matan Chibok 21 sun dawo", inji shugaban yayinda yake misali da irin rawar da kungiyar Red Cross ta taka wajen ba 'yan matan taimakon jin kai a matakin farko. 'Kada a manta 'yan matan sun kwashe kwanaki 900 a hannun wadanda suka sacesu.

Shugaba Buhari yace matsalar da tafi ciwa Najeriya tuwo a kwarya ita ce ta 'yan gudun hijira, wadanda suka rasa muhallansu. Ya lura cewa akwai fiye da mutane miliyan biyu da basa gidajensu. Cikinsu mata da yara sun kai kashi sittin. Cikin yaran wajen kashi sittin basu san iyayensu ba ko kuma inda suke. Yace gwamnati na jin nauyin wannan lamarin.

Dangane da sake gina gidajen da aka ruguza da wasu gine gine da basu yanzu, shugaba Buhari yace abun da gwamnatinsa ta fi ba fifiko ke nan tare da yin la'akari cewa kasashe bakwai mafi karfin masana'antu na duniya da ake kira G7 su sun goyi bayan Najeriya dari bisa dari

Yace "Mun yaba da kokarinku. Na kuma yi farin cikin cewa kun amince sojojinmu na hada kai da kungiyoyin fararen hula kuma suna kare hakin bil Adam. Wannan lokaci ne mai tsanani ma kasar Najeriya. Jihohi 27 cikin 36 ne basu iya biyan albashi ba yayinda muka karbi iko bara, kuma har yanzu muna fama, amma zamu fita daga kangin" inji Shugaba Buhari.

Maurer,shugaban Red Cross yace aikinsu a yankin tafkin Chadi shi ne mafi girma na biyu a duk fadin duniya bayan Siriya. Ya kara da cewa samarda abinci mai gina jiki da magunguna da ruwan sha da tsatace muhalli su ne gimshikin aikinsu a arewa maso gabashin Najeriya.

Yace "Ashirye muke mu bada goyon bayan kawo karshen rikici a Najeriya. Yanzu an fi samun tsaro fiye da shekarar da ta gabata amma har yanzu ana fama da matsalar rayuwa" inji Muerer

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG