Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban PDP Reshen Adamawa Yace Idan Ba Da Addini Ba Kowa Dan Iska Ne


PDP

A wani taron PDP da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Adamawa shugaban jam'iyyar na jiha ya bayyana matakin da zasu dauka akan masu yi masu zagon kasa

Shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa Chief Joel Hamanjore Madaki ya bayyana matakin da zasu dauka.

Yace kowa dan isaka ne. Horaswar iyaye da addini suka canza mutane. Da ya juya kan shugabannin kananan hukumomi sai yace rahoton da suka samu sun nuna cewa suna yiwa jam'iyyar zagon kasa. Haka ma kansiloli. Suna jam'iyyar ne da bakinsu amma zuciyarsu na wata jam'iyyar.

Shi ma gwamnan jihar Bala James Ngilari ya bayyana abun da zasu yi. Kana ya mayarda martani wa wadanda suke cewa bai tabuka komi ba. Yace duk wadanda ba zasu yi Jonathan da Nuhu Ribadu ba su fice daga jam'iyyar tun da sauran lokaci.

Wai da kudi ake cin zabe. Wadanda zasu bada kudin suna nan. Idan an kawo yace zai basu rabonsu su je a yi yakin zabe a kuma ci. Akan 'yan ta'adan Boko Haram yace ko ba'a yaba mashi ba sun koresu saura tashi karamar hukumar.

Shi ma Malama Nuhu Ribadu dan takarar gwamnan jihar a karkashin inuwar PDP cewa yayi suna da shugaban kasa mai son Adamawa. Wai shugaban kasa ya kama bakinsa da ya fada masa cewa babu abun da gwamnatin tarayya tayi a jihar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG