Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasar Najeriya ke Jawo Rikici da Sunan Addini - ra'ayoyin Jama'a


Taron Tattauna Batutuwan Zabe. , Fabrairu 20, 2015.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a wani Zauren Taron Tattaunawar da Murya Amurka ta dauki nauyi shiryawa a Abuja da Kaduna don jin dalilan da ke haddasa yamutsi musamman a siyasar Kasa Najeriya da ta hada mutane masu kabilu da addinai daban-daban.

Mutanen Najeriya na kara samun fargabar barkewar rikicin siyasa kamar yadda ya faru a zaben shekarar 2011 musamman ma yadda ‘yan ta’addar Boko Haram ke dada gyara damarar cikin himmar kai hare-hare, ga kuma yadda siyasar kasar ta ke kara tsamari musamman kan gabatowar babban zaben Kasa a ranar 28 ga watan Maris. Kamar yadda wani dan fafutuka ya fada a Zauren Tattaunawar da Muryar Amurka ta dauki nnauyi a ranar Juma’ar nan.

Fiye dai da mutane 800 ne suka rasa rayukansu biyo bayan rikicin zaben shekarar ta 2011 wanda ya tunkuda Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck kan kujerar shugabancin kasar bayan faduwar tsohon shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari a karkashin juyin mulkin soja a tsakiya karni na alif dari tara da tamanin.

Zanga-zangar magoya bayan Buharin ce ta rikide zuwa zubar da jinin mutane da sunan addini da bangaranci, kasancewar Jonathan kirsitane daga yankin Neja Delta mai arzikin man fetur a kudancin kasa, a yayin da shi kuma Buhari musulmi daga Arewacin Najeriya wanda yake da rinjayen magoya baya a bangaren.

A bana din nan ne dai Buharin ke sake kalubalantar Goodluck dan jam’iyya mai mulki ta PDP game da takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar adawa ta APC. Sai dai hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta dage zaben daga ranar 14 ga Fabrairu zuwa 28 ga watan Maris din bana, wanda hakan yana ci gaba da harzuka bangaorin.

Danjuma Bello shugan matasa ne da ya taba tsunduma a tawagar yakin neman zaben Gwamna a Jihar Kaduna ya fadawa Zauren Tattaunawar da Muryar Amurka ta dauki nauyi cewa, yansiya da ne abin zargi don suna kara iza wutar rikicin zaben siyasa. Inda yace dimbin ‘yan siyasa cewa, “Idan da ‘yan siyasa zasu yi abinda ya dace da duk wannan rikicin zabubbukan sun zama tarihi”. Ya kara da cewa su daina kawo addini ko kabilanci a siyasa, su bar mutane su zabi mutanen da suke so bisa cancanta.

Taron ya gudana ne a Abuja da kuma Kaduna wanda a kiyasance mutanen birnin sun wuce miliyan biyu sannan sun ga tashe-tashen hankulan siyasa a 2011. Umar Yahaya ma ya jagoranci wani yakin neman zaben jam’iyyar APC a Kaduna inda yace, “zaben 2011 yana cike da kura-kuran da suka jawo rikici sakamakon rashin ingancin kidayar kuri’un da ya birkita sakamakon zaben”. Daga karshe ya yabawa hukumar zabe a wannan shekarar yayi kuma fatan a yi zabe a gama lafiya a ranar ta 28 ga watan Maris.

Najeriya ce kasa mafi sanuwa da kuma karfin tattalin arziki a nahiyar Africa. Su ne manyan masu safarar fitar da man fetur ga kasar Amurka zuwa wasu sassan duniya na daban. Ba a Afirka ta Yamma kawai daidaiton Najeriya ya dam aba har ma da sauran nahiyar ta Afirka. Sai dai cin hanci da rashawa tare da kokawa da ‘yan Arewa da mafi yawa musulmai ne suke yawan yi game da tilawa ‘yan kudancin kasar da suke kiristoci ne romon arzikin man fetur ya dabaibaye ci gaban kasar. Kungiyar Boko Haram an fito da ita ne asali don yakar rashawa kafin daga bisani ta rikide zuwa ta ta’addanci.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG