Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Philippines Ya Alakanta Kansa da Hitler


Shugaban Philippines Duterte wanda yake kashe masusha da sayar da kwayoyin sa maye

A yau Juma’a, shugaban Philippines, Rodrigo Duterte, ya alakanta kansa da shugaban Nazi Adolf Hitler, inda ya ce, zai yi farin ciki idan ya kashe masu mu’amulla da muggan kwayoyi da masu aikata miyagun laifuka miliyan uku, inda ya ce yin hakan wata hanya ce da za ta kawo karshen wadanna matsaloli.

Shugaba Duterte, wanda ya nemi majalisar dattawan kasar ta tsawaita wa’adin da suka bashi na yaki da masu mu’amulla da muggan kwayoyi, ya ce sukar da masu kare hakkin bil’adama ke yi, ba zai hana shi ci gaba da yakar masu shan muggan kwayoyin ba.

“Hitler ya kashe yahudawa miliyan uku, muna da masu shan muggan kwayoyi miliyan uku, zan yi farin ciki idan na kashe su.” Shugaba Duterte ya ce a birnin Davao bayan wata ziyara da ya kai Vietnam.

A lokacin jawabin, shugaban na Philippines, ya yi biris da Amurka da kasashen Turai, inda ya ce in sun ga dama su kirashi duk abinda su ke so.

A watan Yunin wannan shekarar nan, shugaba Duterte ya dare karagar mulkin kasar, bayan da ya lashe zaben a watan Mayu, ya kuma sha alwashin sai ya ga bayan matsalar cin hanci da rashawa da masu safarar muggan kwayoyi a kasar ta Philippines mai yawan jama’a miliyan 100.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG