Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Somaliya Ya Nada Sabon Firayim Minista


Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, Farmajo,
Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, Farmajo,

Sabon shugaban Somaliya ya zabi wani shugaban kamfanin mai kuma tsohon darektan wata kungiyar agaji a matsayin sabon Firayim Ministn kasar.

An dora ma Hassan Ali Khaire alhakin karfafa gwamnatin tarayya ta Somaliya tare da maido da kwanciyar hankali a wannan kasa dake fama da farmakin ‘yan kishin islama da kuma rashin ruwan sama.

A yau Alhamis shugaba Mohammed Abdullahi Farmajo ya bayyana nadin a shafinsa na Twitter.

Khaire ya shafe shekaru biyu da rabi da suka shige yana rike da mukamin Darekta mai kula da Afirka na kamfanin man kasar a Britaniya mai suna Soma Oil & Gas. Daga 2011 zuwa 2014 kuma, shine darekta mai kula da yankin gabashin Afirka na Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway.

A shekarar 2013, gwamnatin Somaliya ta damkawa Khaire aikin binciko man fetur da gas a cikin tekun gabar Somaliya.

Khaire mai shekaru arba’in da wani abu, sabon shiga ne a harkokin siyasar Somaliya. Amma wadanda suka san shi sun yaba da iya maganarsa, suka kuma ce yana da dangantaka mai kyau da shugabannin yankunan kasar Somaliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG