Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan ta Kudu Da Madugun 'Yan Tawaye Sun Hadu a Ethiopia


Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar yayinda ya isa Ethiopia
Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar yayinda ya isa Ethiopia

A karon farko cikin shekaru byu shugaban Sudan ta Kudu Silva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar sun hadu a wani yunkurin Firai Ministan Ethiopia na sasantasu

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da shugaban ‘yan tawaye Riek Machar sun hadu gaba-da-gaba a jiya Laraba, wadda ita ce haduwarsu ta farko cikin shekaru biyu.

Taron wanda aka yi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, na zuwa ne, a matsayin wani yunkurin da ake yi na kawo karshen shekaru biyar da aka kwashe ana yakin basasa a Sudan ta Kudu, wacce ita ce ‘yar autar kasashen Duniya.

Rikicin ya lakume rayukan dubun dubatar mutane, kana ya tilastawa kusan mutane miliyan hudu ficewa daga gidajensu.

Ya zuwa yanzu ba san sakamakon wannan ganawa da shugabannin biyu suka yi ba, amma kuma masu lura da al’amura na ci gaba da sa ido kan ganawar.

Wata babbar jami’a mai fashin baki a kungiyar da ke bincike kan rikice-rikicen da ake samu a sassan Duniya mai suna Casie Copeland, ta ce, har shugaba Kiir da Machar suka fice ba tare da an cimma wata matsaya ba, hakan zai dora alamar tambaya akan kungiyar raya kasashen yankin ta IGAD, mai dauke da mambobin kasashe takwas, kan ko tana da tagomashin da za ta iya sasanta wannan rikicin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG