Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Yamal ya kori mataimakinsa da firayim ministan kasar daga mukamansu


Shugaban Yemal Abed Rabbo Mansour Hadi

Jaridun kasar Yamal sun bayyana cewa, Shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi ya kori Fira-Minista da Mataimakin Shugaban Kasar Khalid Bahah, a wani babban sake lalen gwamantin kasar gabanin tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya ko MDD kan zaman lafiya tsakaninsa da ‘yan Shi’ar Houthi da Iran ke marawa baya da za’a fara ran 18 ga Afrilun nan a Kuwait.

Gidan talbijin din kasar ya bada rahoton cewa, Shugaban ya nada wani Janar Ali Mohsen Al-Ahmar a matsayin mataimakinsa da kuma nada wani Dan Majalisa Ahmed Obeid Daghr a matsayin Firayim Ministan kasar.

Har zuwa safiyar Litinin din nan dai Abd-Rabbu bai bada wani dalilin canza mutanen ba, to amma kafafen yada labaran Yamal da na kasashen duniya sun bada rahoton yadda ake allan-baku tsakaninsa da Bahah game da yadda za’a tsara kawo karshen dogon yakin basasar kasar.

Hakan ya fito ,fili ne a watan Disambar bara, lokacin Bahah din yaki yarda da sake lalen wasu lamuran gwamnati ba tare da an fara tuntubarsa ba. Wanda aka yi ammar cewa shi mai son ayi abu a siyasance ne ba kamar Shugaba Mansour Hadi da ya kan so tursasawa ba. Fiye dai da mutane Dubu 6 ne suka halaka a yakin na Yamal.

XS
SM
MD
LG