Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban 'Yansandan Las Vegas Na Zaton Za'a Gano Dalilin Kisan Kan Ranar Lahadi


Daliban Jami'ar Nevada ta birnin Las Vegas suna juyayin wadanda aka kashe aranar Lahadi
Daliban Jami'ar Nevada ta birnin Las Vegas suna juyayin wadanda aka kashe aranar Lahadi

Duk da matsalar da masu bincike suke fuskanta shugaban 'yansandan birnin Las Vegas nada karfin gwuiwar za'a gano musabbabin kisan kan da Stephen Paddock yayi wanda shi ne ya fi muni a tarihin Amurka

Shugaban ‘yan sandan Las Vegas, Joseph Lombardo, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa, masu bincike za su gano ainihin dalilin da ya sa aka samu aukuwar kisan kai na dumbin jama’a da ya fi muni a tarihin Amurka.

Masu binciken kamar yadda rahotannin suka nuna, sun tsinci kansu cikin zurfin tunani a kokarin gano dalilin da ya sa Stephen Paddock mai shekaru 64, wanda yake da arziki kuma ba shi da tarihin aikata wani laifi ko alaka da wata kungiyar siyasa ko ta addini, ya bude wuta akan wani taron shagalin wake-wake a daren Lahadin, inda ya halaka mutane 59, har da kansa, ya kuma jikkata wasu 527.

Yayin wani taron manema labarai da aka yi a jiya Talata, Lambardo ya ce, ga dukkan alamu, wannan kashe-kashe da ya aikata ya shirya shi da kyau, yana mai cewa Paddock sai da ya auna duk abinda ya aikata.

Wani jami’in hukumar tsaron cikin gida, ya ce ba za a kore yiwuwar cewa ya samu tabin hankali ba ko kuma kwakwalwarsa ta samu matsala, duk da cewa babu wata alama da ta nuna haka.

Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun samu jumullar bindigogi 47 daga wurare uku da suka hada da dakin otel dinsa da gidansa dake Mesquite da Verdi duk a jihar ta Nevada, sannan an samu dumbin harsashai da ababan fashewa a cikin motarsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG