Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zimbabwe Ya Koma Gida Saboda Tsananin Rikicin Kasar


Zimbabwe's President Emmerson Mnangagwa speaks during a meeting with Belarus' President Alexander Lukashenko in Minsk, Belarus, Jan. 17, 2019.
Zimbabwe's President Emmerson Mnangagwa speaks during a meeting with Belarus' President Alexander Lukashenko in Minsk, Belarus, Jan. 17, 2019.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya takaita ziyararsa ta kasa da kasa ya koma gida jiya Litinin, bayan kwanaki da aka yi ana zanga zangar adawa da gwamnati da ta hallaka akalla mutane 12.

An fara zanga-zangar a makon da ya gabata bayan da Mnangagwa ya sanar da Karin farashin man fetur da kashi 150.

Yayin da zanga-zangar ta yi tsamari, Mataimakin Shugaban kasar Constantino Chiwenga, tsohon kwamandan soji, ya kaddamar da wani mummunan farmaki wanda ya sa jami'an tsaro suka harbe masu zanga-zangar da kuma jawo mutane daga gidajensu ana dukan su, a cewar 'yan gwagwarmaya.

A ranar Laraba da ta gabata, jami'an tsaro sun harbe mutane biyar kuma sun jikkata 25 a babban birnin kasar Harare, a cewar ‘yan Adawar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG