Accessibility links

Shugabanci Nagari Shi Zai Kawo Daidaituwa A Najeriya


Goodluck Jonathan shugaban Najeriya

A Taron samarda shugabanci nagari da aka gudanar Farfasa L. A. Adeyemi ya ce muddin shugabanni basu kawar da son rai ba to kasar zata cigaba da zama cikin rudani da komawa bayan a duk fannin rayuwa.

Najeriya na bukatar shugabanni nagari wadanda basu da son zuciya idan har kasar zata samu ta cigaba.

A taron samarda shugabanci nagari da ya wakana a Legas Farfasa L. A. Adeyemi a cikin kasidar da ya bayar ya ce muddin kasar bata samu shugabanni nagari ba to wutar rikicin kasar zata cigaba da kara ruruwa. Taron da mujallar Lead ta shiya yana da nufin jawo hankulan shugabannin kasar a kan matsaloli daban-daban da suka yiwa kasar katutu. Farfasan ya ce matsala guda ta isa ta takure kasa balantana a ce suna da yawa.Sabili da haka irin wannan taron na tunawa shugabannin ne domin su ma mutane ne sai ana yi ana tunashesu da matsalolin da suka addabi kasar.

Abubuwan sawun farko da ya kamata shugabnni su tunkara su ne harkokin tsaro da samar ma matasa ayyukan yi da samarma jama'a abubuwan more rayuwa da cusa dabi'un da'a ga jama'a muddin suna son kasar ta sami cigaba mai ma'ana. Ya ce shugabannin su yi kokarin kankare kabilanci da ban-bancin addini da shiya ko siyasa hakan zai sa 'yan kasa su rika kallon kansu 'yan Najeriya kafin duk wani abu.

To da yake taron ya samu halarcin kusan duk jama'a daga kowane sashin Najeriya Alhaji Adamu Bomboy ya ce a matsayinsa na dan Najeriya shi bai san wani shugaba ba in ba gwamna dake yawo da jiniya ba. Tun zaben kananan hukumomi da aka yi a shekarar 1999 ba'a sake yin wani ba sai dai gwamna ya nada shugaban riko kowane wata shida- shida. Albashin shugaban hukuma da aka nada nera dubu darine da nera miliyan biyu na kashewa. Idan za'a fara baiwa kananan hukumomi kudi kai tsaye daga Abuja to gara mutum ya zama shugaban karamar hukuma da zama minista. Ya ce idan ka zama shugaban karamar hukuma ka iya gina rijiyoyin burtsatsin ruwa guda biyar cikin kowane wata shida.

Wani matashi daga arewacin Najeriya ya ce matsalolin da suka addabi Najeriya tun lokacin samun 'yanci su ne suke damun kasar har yanzu. Har yanzu akwai matsalar . wutar lantarki. Akwai matsalar hanyoyi. Akwai matsalar rashin magunguna a asibitoci. Makaranatu sun lalace. A ce shekaru fiye da hamsin da samun'yancin kai yara suna daukan darusa a kasa ko karkashin bishiyoyi.

Kusan duk wanda ya yi magana a taron ya danganta matsalolin Najeriya da rashin shugabanci nagari.

Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG