Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addini Sunce Sai sun Cusa Halin Daa Ne Ga Jama'a Kasa Zata Gyaru

Wata Kungiyar Shimfidar Karfafa Kan Addinai ta hada shugabannin matasan addinai daga addinin Islama da na Krista a Abuja domin ta taimaki inganta zaman lafiya musamman a arewacin Najeriya.
Wata Kungiyar Shimfidar Karfafa Kan Addinai ta hada shugabannin matasan addinai daga addinin Islama da na Krista a Abuja domin ta taimaki inganta zaman lafiya musamman a arewacin Najeriya.

Amma sakataren kungiyar kiristoci jihar Niger Reverend Joshua cewa yayi kamata yayi malaman addinan su mayar da hankali wajen cusawa jamaa jin tsoron ALLAH.

A yayin da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ke fafutikar shawo kan tashin hankali kungiyar boko haram a Najeriya shugabannin addinai naci gaba da bada shawarwarin gano bakin zaren.

Sarkin Malaman jihar Niger Alhaji Mammam Da Mariga cewa yayi gudanar da adduoi na musammam a kasa a dai dai wannan lokacin da rikicin boko haram ke kara zafi nada matukan tasiri.

‘’To don ALLAH don ANNABI malamai da kiristoci a neme su ko wane yayi addua a mujamiaar shi, a nemi wadanda zasu tsaya suyi addua tsakani da ALLAH, ALLAH shi kawo muna karshen wannan balai’’

Amma sakataren kungiyar kiristoci jihar Niger Reverend Joshua cewa yayi kamata yayi malaman addinan su mayar da hankali wajen cusawa jamaa jin tsoron ALLAH.

‘’ Kai abinda ya kamata muyi Shine malamai addinan nan suyi gaskiya domin idan ba muyi gaskiya ba, idan bamu koya ma mutane ainihin nufin ubangiji ba to lallai kam zasu bijire kuma na fada maka dazu cewa duk wanda bashi da jin tsoron ALLAH , to yafi dabba muni domin hankalin sa ban a irin mutane bane’’

Ga Dai Mustafa Nasir Batsari da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG