Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin ECOWAS Na Ci Gaba Da Kokarin Sasanta Rikicin Mali


Taron ECOWAS A Mali
Taron ECOWAS A Mali

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma za su yi wani taron koli ta yanar gizo ranar Litinin 27 ga watan Yuli don gabatar da matakan kawo karshen rikicin siyasar kasar Mali da ke kara muni, bayan da wasu Shugabannin kasashe biyar na kungiyar suka gana da gwamnatin Mali da bangaren ‘yan adawa a Bamako babban birnin kasar ranar Alhamis 23 ga watan Yuli.

Jagoran kungiyar kasashen ECOWAS, Shugaba Mahammadou Issoufou na Nijer, ya ce kungiyar kasashen na yammacin yankin Afrika za ta yi duk abinda ya dace don sulhunta rikicin siyasar da ke faruwa a Mali, a cewar wata sanarwar da gwamnatin Najeriya ta tura wa manema labarai.

Taron da aka yi ranar Alhamis, wanda ya samu halarcin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita mai masaukin baki, da Shugaba Machy Sall na kasar Senegal, da Nana Akufo -Addo na Ghana, da Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire, sun saurari jawabai daga wakilin ECOWAS na musamman tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da kuma madugun ‘yan adawar Mali Imam Mahmoud Dicko, da wakilan hadakar ‘yan adawa, da kuma kungiyoyin al’umma.

Shugaban Mali ya yi wa Shugabannin kasashen jawabi game da yanayin zamantakewa da siyasar kasar, musamman rashin jituwar da aka samu da ta kai ga zanga-zanga da tashin hankali.

Keita ya ce Shugabannin na ECOWAS sun riga sun amince da cewa akwai bukatar a cimma yarjejeniya don kiyaye zaman lafiya da mutuncin kasar, ya kara da cewa barin rikicin siyasar Mali ya kara tsananta zai iya shafar yanayin tsaro a yankin Afrika ta yamma, musamman kasashe makwabtan Mali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG