Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin kasashe masu wadatar masana’antu a duniya, sun fara taron kolin G20 a birnin Cannes na Faransa


Shugaba Barack Obama a gefen hagu ke tattaunawa tare da shugaba Nicolas Sarkozy na faransa na G20 a Cannes, kasar Faransa.
Shugaba Barack Obama a gefen hagu ke tattaunawa tare da shugaba Nicolas Sarkozy na faransa na G20 a Cannes, kasar Faransa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana a kebe tare da shugabar kasar Faransa Nicolas Sarkozy da shugabar kasar Jamus Angela Merkel, wadanda ke zama a sahun gaban kasashen turai da tattalin arziknsu keda karfi.Anyi tattaunawar ce a taron kolin G-20 da aka fara Alahmis. Shugaba Obama yace tarayyar Turai na daukan kwararan matakai domin maganta matsin lambar yawan bashin dake kan Amurka, kuma yace akwai fatan taron kolin kasashe masu arzikin da ake yi yanzu zai taimaka da muhimman shawarwarin kaiwa ga warware matsalolin tattalin arzikin kasa da kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG