Accessibility links

Mutum 6 Sun Mutu A Harin Bom Din Da Aka Kai Kasuwar Baghadaza

  • Halima Djimrao-Kane

'Yan kwana-kwana na kashe gobara a kasuwar Shurja ta birnin Bgahadaza wadda aka kaiwa harin boma-bomai Lahadin nan ranar Sallar Layya

Boma-boman da suka fashe a kasuwar Shurja ta birnin Baghadaza, sun janyo gobara a wani gefen unguwar

Jami’an gwamnatin kasar Iraqi sun ce wasu fashe-fashe har guda ukku sun girgiza wata kasuwa mai hada-hada a Baghadaza babban birnin kasar, sun halaka mutum 6 a kalla, wasu kuma fiye da 20 sun raunata.

Fashe-fashen boma-boman da suka wakana a kasuwar Shurja ta birnin Baghadaza, sun janyo gobara a wani gefen unguwar ta kasuwanci a yau Lahadi ranar da Musulmi ke Sallar Eid al-Adha ko Sallar Layya.

Yawan tashe-tashen hankula sun ragu a kasar Iraqi, amma har yanzu kusan a kowace rana ana ci gaba da samun munanan hare-haren da ke kisa, hakan kuwa a daidai lokacin da Amurka ke shirin janye duka sojojin ta dubu 33 daga kasar a karshen shekara.

Wasu sojojin Amurka da ke kasar Iraki sun yi layi zasu shiga bas
Wasu sojojin Amurka da ke kasar Iraki sun yi layi zasu shiga bas

XS
SM
MD
LG