Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kungiyar Kasashen Afirka Sun Kasa Zaben Wani Babban Matsayi


Shugabannin kasashen cikin kungiyar Tarayyar Afirka a wurin taron

Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun kasa zaben

Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun kasa zaben sabon Shugaban Hukumar Zartaswa ta kungiyar a yau dinnan Litini, a wurin taron kungiyar a Addis Ababa.

A zaben, an ja daga a babban birnin kasar Habasha tsakanin Shugaba mai ci, Jean Ping na kasar Gabon, da kuma Ministan Muhalli na Afirka ta Kudu Nkosazana Dlamini-Zuma.

Komai ya cije bayan zango uku na zaben, ta yadda babu ko daya daga cikin ‘yan takarar da ya sami kashi biyu bisa ukun da ake bukata kafin a ci.

Mataimakin Hukumar Zartassa ta kungiyar ta AU Erastus Mwencha dan asalin kasar Kenya, zai maza Shugaban wuccin gadi kafin a yi sabon a zabe cikin watan Yuni. Wannan hukumar dai ita ce fannin zartaswar kungiyar AU, wadda ke kula da sha’anin kasuwanci da tsaro da kuma sauran abubuwan da su ka shafi manufofin kungiyar.

Shugabannin kasashen cikin kungiyar sun fara aiwatar da maudu’in taron a jiya Lahadi da zaben Shugaban kasar Benin Thomas Yayi Boni a mtsayin Shugaban AU daga badi.

A taron na kwanaki biyu, an kuma bayar da hankali kan takaddamar arzikin man fetur tsakanin Sudan da sabuwar kasar Sudan ta Kudu, da kuma tashin hankalin kasar Somaliya da yaki ya daidaita.

XS
SM
MD
LG