“Mu na da kwakkwarar dama da zamu iya rufe hanyar nan ta tekun Meditareniya,” a cewar shugaban Majalisar kungiyar ta EU, Donald Tusk, yayin da yake ganawa da manema labarai a taron kolin da aka yi a Brussels.
Bayanin na Tusk na nuni ne da tsallaka tekun Meditareniya mai cike da hadari da bakin haure ke yi tsakanin Libya da Tsibirin Lampedusa da ke Italiya – mashigi na farko da bakin na haure ke isa a nahiyar ta turai.
Dubban mutane ne suke halaka yayin da suke kokarin tsallaka tekun a cikin jiragen kwalekwale marasa inganci, ko kuma idan masu safarar mutanen sun yasar da su akan tekun.
Hukumomin Italiya sun ce adadin bakin hauren da ke tasowa daga Libya ya ragu da kashi 20 cikin 100 a bana, tun bayan da suka hada kai da takwarorinsu na Libya wajen dakile kwararar bakin hauren.
Facebook Forum