Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Tarayyar Turai Zasu Yi Taro Kan 'Yan Gudun Hijira


Federica Mogherini, shugabar huldar siyasa ta kasashen turai

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai za su yi taro a gobe Laraba game da yadda maganar ‘yan gudun hijira ke rarraba kawunan su.

Shugabar huldar siyasar kasashen waje na kungiyar Federica Mogherini ya bukaci da Ministocin na Turai da su daina cin diddigen maganar rarraba ‘yan gudun hijirar a Turai.

Majalisar dokokin kasar Hungary ta umarci sojojin kasar da ta yi amfani da makamin da ba zai kai ga halaka ba wajen hana shigar ‘yan gudun hijira cikin kasar ba bisa ka’ida ba.

Kasar dai tuni da datse kan iyakarta da Serbia ta hanyar sa shingen waya mai kaifi. Sojojin na Hungary za su iya amfani da harsashin roba ko barkonon tsohuwa da makamantansu.

Suna ma iya caje gida-gida don farautar bakin hauren ba bisa ka’ida ba. Sauran kasashen tarayyar Turai sun yi tir da yadda Hungary ke wa ‘yan gudun hijirar.

Inda suka cewa kasar na amfanin da dabarun karfa-karfa irin wadanda ‘yan Nazi suka yi amfani da shi a baya.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG