Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Rasha Da Syria Suna Gab Da Daukan Mataki


Russia Syria
Russia Syria

Shugaba Vladmir Putin da shugaba Bashar Al Assad sun tattauna a garin Sochi a Rasha kan matakan da za a iya dauka na warware rikicin kasar Syria ta hanyar lumana.

Shugaban kasar Russia Vladmir Putin da shugaban Syria Bashar Al Assad sun tattauna a garin Sochi akan bukatar mai da hankali wajen magance rikicin kasar ta fuskar Siyasa. Jiya Litinin ne shugabannin suka tattauna a birnin Sochi, a wata ganawar da ba'a bada labarin ta ba.


A yau talata kasashen guda biyu suka bayyana batun zaman da suka yi. Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, yace tattaunawar zata taimaka wajen tabbatar da dorewar duk wata yarjejeniyar da Rasha ta kulla da shugabannin Turkiyya da kuma Iran.


Kafofin yada labaran Russia da Syria sunce Putin ya bayyana cewa an kusa zuwa karshen matakan soji a Syria, kuma ya taya shugaba Asad murna akan nasarar da yayi ta yaki da 'yan ta'adda a kasar. Assad wanda a cewar kafafan yada labaran Rasha ya je Sochi na tsahon sa'o'i hudu a ranar Litinin, rabon da Assad yaje Rasha tun shekaru biyu da suka wuce a lokacin da jami'am tsaron Rasha suka dauki matakin soji a Syria da suka taimakawa sojojin na Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG