Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SIERRA LEONE: An Gano Kwayar Cutar Ebola a Wata Gawa


Adama Sankoh wadda ta kamu da kwayar cutar daga gawar danta
Adama Sankoh wadda ta kamu da kwayar cutar daga gawar danta

Jami’an kiwon lafiya a kasar Saliyo sun tabbatar da wata mutawa da take alaka da cutar Ebola, ‘kasa da mako daya da sallamar mutum na karshe a kasar dake da cutar daga asibiti.

Brima Kargbo wani babban jami’an lafiya yace, an gano alamar cutar a gawar wata macce mai shekaru 67, wadda ta mutu a wani kauye dake kusa da iyakar Gini da ita Saliyon. Kargbo dai ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ana cigaba da bincike domin tabbatar da hakan.

Cibiyar kula da cutar Ebola ta Saliyo tace, tana bin diddigin duk mutanen da suka kusanci matar.

24 ga watan Agusta dai shine ranar karshe da aka sallami mutum na karshe da aka sani da cutar ta Ebola, hakan ne yasa aka fara lissafa kwanaki 42 da ake bukata kafin a tabbatar da kasar a matsayin kasar da ta dakile cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace sama da mutane dubu 11 da 300 a kasashen Saliyo da Gini da Laberiya ne suka mutu daga cutar Ebola, sama da kashi ‘daya cikin uku na dukkan mutanen kasashen yammacin Afirka da suka kamu daga cutar.

XS
SM
MD
LG