Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sikari Ke Kawo Ciwon Zuciya, Ba Man Kitse Ba

Sikari
Sikari

Fiye da shekaru 60, yawancin hukumomin lafiya sunyi gargadin amfani da kitsen naman dabbobi cewa yana kawo cutar zuciya da kuma dole a rage shi daga abinci na zuciya. Amma bisaga wani sabon bincike da aka baiyyana a maganin JAMA, cewa sikari shine ainihin abinda ke kawo cutar zuciya ba kishen naman dabbobi ba.

Wani binciken mutane fiye da 40,000 ya baiyyana cewa a wadansu yanayi, yawan shan sikari yana kawo kashi 400 na hadarin cutar zuciya. Wannan binciken ya nuna cewa hadarin cutar zuciya yana karuwa idan sikari ya kai kashi 20 na abinda mutum ke sha.
Bisaga masu bincike, wannan sabon binciken na nuna yadda sikari ke kawo raguwar sinadarin dake rage yawan sikari cikin jinni kuma shi ke kara wuta, wanda likitoci yanzu suka sani cewa shine tushen cutar zuciya. Banda wani irin kitse maisuna trans, yawancin kitse basu da hadari.

Wannan ya hada da kitsen Omega-3, man gyada, wanda aka tabbatar ya rage hadarin cutar zuciya fiye da kashi 30 a binciken kwanannan wanda akayi cikin jama’a da yawa.

Ga cikakkiyar gaskiyar: kaloris na sikari yafi kowanne kaloris hadari. Dukan kaloris ba daya suke ba. Wani bincike na kwanannan, na fiye da kasashe 175, ya nuna cewa karuwar kaloris bai kara hadarin Type 2 na ciwon siga ba, amma karuwar sikari yayi sosai.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG