Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Amurka Ta Janyo Faduwar Hanayen Jari A Kasashen Turai Da Nahiyar Asiya


Wasu 'yan siyasa na ganin matakai da kalaman masu cike da takaddama na shugaba Donald Trump zasu kawo mashi cikas a harkokin siyasar sa

Hannayen jari a kasashen Turai da nahiyar Asiya sun fadi, kwana daya bayan da hannayen jarin Amurka, da dalar kasar suka fadi, a daidai lokacin da masu sanya hannayen jari ke nuna damuwa akan matakai da kalamai masu cike da takaddama dake fitowa daga bakin shugaba Donald Trump.

Alkaluman darajar kudi da cinikayya na Amurka sun nuna an sami faduwar darajar da kashi 1.8 ko ma fin haka a jiya Laraba.

Faduwar hannayen jarin na faruwa ne bayan korar shugaban hukumar binciken sirri ta FBI da Trump yayi, da kuma zargin da akewa shugaban na cewa ya bada bayanan sirri ga manyan jami’an Rasha, da kuma ma zargin cewa shugaban ya yi kokarin ya dakatar da binciken wani babban jami’insa da aka kora kwanan baya, wato Michael Flynn.

Darajar dalar kasar da kuma hannayen jari sun cilla sama sosai, bayan zaben Trump, saboda kwarin gwiwar da masu sanya hannun jari ke dashi akan cewa shugaban zai cika alkawalin rage haraji, kuma tsare-tsaren da zai fito da su na kasuwanci zasu bunkasa tattalin arzikin kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG