Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Jari Hujja Ta Nakkasa Tattalin Arziki Da Sanin Ya Kamata A Najeriya - Masu Sharhi


Yan Siyasar Najeriya Sun Garkame Kofofin Shiga Majalisar Dokoki
Yan Siyasar Najeriya Sun Garkame Kofofin Shiga Majalisar Dokoki

Duk da tsarin dimokradiyya da a ke yi a Najeriya, masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya ba, don tsarin jari hujja da ke nisanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.

Masu nazari kan lamuran yau da kullum a Najeriya da su ka hada da masana tarihi na dora alhakin koma bayan tattalin arziki da sanin ya kamata kan nasarar da ‘yan jari hujja su ka samu na amshe madafun iko da fakewa da cewa gyara su ke yi.

Duk da tsarin dimokradiyya da a ke yi a Najeriya, masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya ba, don tsarin jari hujja da ke nisanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.

Masana siyasa na karfafa batun nan da ke cewa siyasa tamkar kasuwar bukata ce, kowa na shiga don samun abun da ya ke muradi, don haka ba a samun makiyi ko masoyi na dindindin.

Bai zama abun mamaki ba a ‘yan kwanakin nan da ake ganin manyan ‘yan siyasa da a baya ba sa ga maciji da juna amma yanzu sun hade, duk da dama a bayan fage matansu kan yi hulda da juna inda su kan bar talakawa masu mara baya da wanzar da hamaiya ko ma kiyaiyar.

A lokacin yakin neman zabe a kan samu matasa talakawa da ke marawa sassa biyu na ‘yan jari hujja na arangama da juna alhali iyalan gwanayen su na can kuryar daki ko kasashen ketare su na karatu ko yawon shan iska.

Masanin tarihi Muhammad I. Usman ya ce tuni ‘yan siyasa da dama suka sauka daga turbar da magabata su ka aza kasar tun 1960-1966.

Shi kuma Sheikh Hussein Zakariyya ya ce rashin samar da muhimman abubuwan more rayuwa, ya sa ‘yan jari hujja takaita ribar dimokradiyyar a gidajensu ko anguwannin su na GRA.

Musamman gwamnatin APC mai ci na cewa ta na tsayin dakan gyaran lamuran da su ka tabarbare ne a zamanin gwamnatocin baya da ba su yi fama da faduwar darajar fetur ko annobar korona bairos ba.

Tun faduwa zaben PDP a shekarar 2015 da ya kawo hawa mulkin gamaiyar ‘yan adawa, Najeriya ta tsira daga mulkin jam’iyya daya, don haka ko banza dukkan sassa biyu sun dana mulki, wadanda su ka saura a bayan fage su ne ‘yan bama can ba ma nan.

XS
SM
MD
LG