Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojan Najeriya tace ta tarwatsa wani yunkurin kai farmaki na mayakan Boko Haram


Dakarun Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko
Dakarun Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko

Sojojin Najeriya sun tarwatsa wani yunkurin kai harin ta’addanci da mayakan Boko Haram suka shirya kaiwa a Maiduguri a jiya Litinin, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba da ya kai su ga arcewa domin ceton rayuakansu.

Jami’an sojin basu yi Karin bayanin ba a kan wannan yunkurin.

Amma shugaban wata kungiyar ‘yan sa-kai ya fadawa kampanin dillancin labaran Faransa cewa, mayakan sun yi amfani da jerin gwanon motocin fararen hula suna nufin kai hari a kan wani shingen binciken sojoji a wajen Maiduguri inda suka bude wuta a kan sojojin.

Sojojin sun mai da martani da nasu bindigogin. Sojojin sun samu Karin wasu jami’ansu daga cikin Maiduguri da suka kawo musu dauki, inda yan ta’addan suka arce da motocinsu.

Ya zuwa yanzu dai ba’a tantance asarar rayukan da aka yi a cikin fadan ba.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG