Accessibility links

Sojoji A Adamawa Sun Kama Masu Safarar Muggan Makamai


Hotunan wani wurin da kungiyar Boko Haram ke harhada boma bomai a Mariri Quarters dake karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano

Kama mutanen ya biyo bayan damke wani dan sanda mai suna Reuben Joel bisa zargin yana sayarwa da 'yan ta'adda rigunan soja da na 'yan sanda

Sojoji a Jihar Adamawa a Najeriya, sun kama wasu gungun masu fataucin muggan makamai tare da sayar da rigunan soja da na ‘yan sanda ga masu aikata laifi.

Wakilin Muryar Amurka a Yola, Ibrahim Abdulaziz, yace wadanda aka kama sun hada da wata mace mai suna Nancy James da wani mai suna Haliru Jumba, wanda aka ce Pasto ne na wata majami'ar Deeper Life a wani gari dake karamar hukumar Lau, cikin Jihar Taraba.

Damke wadannan dillalan bindigogin yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin a Jihar Adamawa suka kama wani kofur na ‘yan sanda mai suna Reuben Joel, a garin Mubi, bisa zargin yana sayar da rigunan sojoji da na ‘yan sanda ga ‘yan ta’adda.

Shi wannan dan sanda, Kofur Reuben Joel, yana aiki ne a rundunar yaki da ta'addanci ta 'yan sanda a Aba, Jihar Abia, amma sojojin runduna ta 23 dake Yola sun ce sun damke shi ne a garin Mubi yana aikata abinda suke zargin nasa.

XS
SM
MD
LG