Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Na Luguden Wuta Ba Kakkautawa Kan 'Yan Bindiga A Zamfara


Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai.
Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai.

Gwamnatin jihar Zamfara ta rurrufe dukkan kananan tashoshin mota da ke kan tituna, a yayin da dakarun sojin Najeriya suka zafafa luguden wuta kan ‘yan bindigar daji a jihar.

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da luguden wuta da ruwan bama-bamai kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Zamfara, a wani yunkuri na dakile ayukan tada kayar baya da ke neman shige makadi da rawa a jihar.

Hakan na zuwa ne kwanaki 3 bayan da aka rufe dukkan kafofin sadarwa, kasuwanni da ma wasu manyan tituna, tare kuma da takaita zirga-zirga a jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan watsa labaran jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar, ta ce sojojin sama suna luguden wuta da ruwan bama-bamai ba kakkautawa daga sama kan sansanonin ‘yan bindigar, yayin da su kuma sojin kasa suke bi domin fatattakar wadanda ke neman tserewa a dajin.

Dakarun Najeriya 'yan bindiga a Jihar Zamfara.
Dakarun Najeriya 'yan bindiga a Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu sojojin sun sami tarwatsa wasu sansanonin ‘yan bindigar da suka hada da dabar shahararren jagoran ‘yan ta’adda da aka fi sani da ‘Dankarami’ a karamar hukumar mulki ta shinkafi.

A ‘yan watannin baya ne wani hoton bidiyo ya karade kafafen sada zumunta na yanar gizo, da ke nuna Dankarami tare da mabiyansa suna bikin murnar samun galaba kan sojoji a cikin daji.

A29 SUPER TUCANO
A29 SUPER TUCANO

Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun soma kwararowa cikin gari domin gudun tsira da rai sakamakon ruwan wutar da sojoji ke yi a sansanoninsu.

Akan haka ne gwamnatin jihar ta kafa dokar rurrufe dukkan tashohin motar da ke kan tituna, da suka hada da kan titin Kauran Namoda-Jibiya, mahadar titin Lambar Bakura, mahadar titin Anka a Kwanar Mayanchi, Garejin Mai Lena da kuma babbar kasuwar kayan abinci da na marmari da ke cikin Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

Wannan da shi ne mataki na baya-bayan nan da hukumomi suka dauka na yaki da ‘yan bindigar da suka addabi al’umma da kai hare-hare, kisan jama’a da satar dabbobi da mutane domin karbar kudin fansa a jihar ta Zamfara da ma makwabtan jihohi.

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

XS
SM
MD
LG