Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Ce Rufe Al'amura Zai Kara Karfafawa ‘Yan Bindgiga Gwiwa Ne Kawai


Kungiyar Dattawan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa ta ce umarnin rurrufe hanyoyin sadarwa da matakan rufe kasuwanni da makarantu a jihar Zamfara ba ita ce mafita ga ayyukan yan bindiga ba, a daidai lokacin da jama'ar jihar suke bayyana cewa matakan sun soma haifar da kyakkyawan sakamako.

A cikin wata Sanarwa da Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar ta dattawan Arewa ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa matakan za su iya kara karfafawa ’yan bindigar gwiwar a maimakon dakile ayyukansu.

Kungiyar ta kara da cewa daukar irin wadannan matakan zai jefa tattalin arziki Najeriya cikin matsi da kuma hana walwalar jama’a, sakamakon kakaba sabuwar dokar kulle, idan aka yi la'akari da yadda al’ummar yankin suka dade suna fuskantar matsin rayuwa a hannun hannun ’yan bindigar da ke cin karensu ba bu babbaka.

Ta ce kamata yayi gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su dauki kwakkwaran mataki a kan ’yan bindiga da masu satar mutane domin karbar kudin fansa yana mai cewa muddin ba’a dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba, al’umma za su kara tsunduma ne cikin halin kuncin banda wanda suke ciki.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed
Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Kungiyar ta dattawan Arewa ta soki matakin da gwamnatin jihar Zamfara da wasu gwamnonin yankin Arewa maso yamma suka dauka daya bayan daya a matsayin hanyar kawo karshen yan bindiga da ke ci gaba da addabar al’umma a yankin arewa maso yamma da suka hada da Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Naija da dai sauransu.

Gwamnatocin jihohin na arewa maso yamma dai sun dauki matakin rufe kasuwanni, makarantu da kuma hana zirga-zirga da cinikin dabbobi a matsayin hanyar dakile kalubalen tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin su ne don samo mafita mai dorewa.

A karshen makon da ya gabata ne kuma gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da umarnin rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara, domin baiwa dakarun kasar damar gudanar da wasu ayukan yaki da 'yan bindiga a jihar.

Tuni kuma da al'ummar jihar suka bayyana ra'ayoyin cewa wannan matakin ya soma tasiri, domin kuwa ya soma jefa 'yan bindigar a cikin rudu da ukuba.

Wakilin Muryar Amurka da ke jihar ta Zamfara a lokacin da aka kafa dokokin, ya jiyo wasu 'yan jihar na bayyana cewa 'yan bindigar na fama da matsalar rashin abinci da kuma musamman man fetur da mafi akasari suke amfani da shi domin tafiya wuraren ayukansu na ta'addanci.

Ko a ranar Alhamis da ta gabata an sami rahoton cewa 'yan bindiga sun tare babban titin Gusau zuwa Funtuwa, inda sam ba su damu da sace ko wane mutum ko kaya ba, illa dai kawai suna juye man fetur da ke cikin ababen hawan da suka tare ne kawai.

Haka kuma masu fashin baki kan lamurran tsaro a jihar ta Zamfara, kamar Bashir Muhammad Achida na Jami'ar Usmanu Danfodiyo, ya bayyana cewa rufe kafofin sadarwa a jihar "ya jefa 'yan bindigar cikin duhu na rashin sanin motsin sojoji da sauran jami'an tsaro, ba kamar da ba, da ko kuda ya gitta sai an gaya musu."

XS
SM
MD
LG