Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Ci Zarafin Yara 3,600 A Najeriya - Rahoto


Rahoton Cin Zarafin Yara A Maiduguri
Rahoton Cin Zarafin Yara A Maiduguri

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ta fitar da wani rahoto mai shafuka hamsin da ya yi nuni da cewa Sojojin Najeriya sun kwashi shekaru da dama suna tsare yara kanana da shekarun su bai kai a tsare su ba.

Shugabar tawagar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta kasa da kasa, Jo Becker, ta yi bayani cewa yawancin yaran da suka gana da su sun yi bayanai masu sosa rai, inda su ke cewa ana kama su ne a bisa zargi ko kuma wasu dalilai marasa karfi.

Jo Becker ta bada misalin wani yaro dan shekara 10 da ya ce an kamashi ne domin ana zargin wai yaje ya sayarwa 'yan Boko Haram da doya, sannan daya kuma ana zargin sa ne cewa shi ne yake yi wa ‘yan Boko Haram nune domin su kai hari.

A cewar tawagar wadannan dalilai da ba su taka kara sun karya ba, sun sa an tsare yaran na tsawon shekaru, wannan ya nuna cewa an ci zarafin yaran.

A majigin da aka nuna wa manema labarai, yaran sun koka cewa ana dukan su, kuma har a wurin kwanciya ma sai a hana su juyawa sai dai su kwanta gefe guda, ‘yan mata kuma sunce kan su da jikunan su duk kwarkwata.

A lokacin da ta ke yi mani bayani akan abinda ya dauki hankalinsu akan batun yaran har ta kai ga goyon bayan binciken, Hajiya Hamsatu Al-Amin, ta Kungiyar Al-Amin Foundation For Peace da ke Maiduguri ta ce idan jami'an tsaron suka sako yaran, ana barin su kara zube ne a sansanin ‘yan gudun hijira, sai dai su kai gauro su kai mari don neman na abinci, wani abu da ya kai su gidajen mutane suna aikin wanke wanke, ko goge takalma domin su samu su ci abinci.

Hajiya Hamsatu ta yi kira ga al'umma da mahukunta da su gaggauta daukan matakin tsugunar da yaran saboda a gyara masu dabi'a domin magance abin da ka kai ya komo nan gaba.

Rahoton ya yi bayanin cewa an kama yara dubu 3,600, a ciki akwai mata dubu 1,617 kuma an tsaresu ne a barikin Giwa da ke Maiduguri.

Amma tuni sojojin Najeriya su ka musanta zargin tare da cewa rahoton ba daidai ba ne.

Saurari cikakken rahotan Medina Dauda daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG