Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kama 'Yan Boko Haram 2 A Jihar Borno


Boko Haram Na Tserewa Zuwa Kasashen Tsakiya Da Arewacin Afirka.
Boko Haram Na Tserewa Zuwa Kasashen Tsakiya Da Arewacin Afirka.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sami nasarar kama mayakan kungiyar Boko Haram biyu a yankin Muna da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Brig. Gen. Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an kama ‘yan ta’addar ne a wani samame da rundunar nan ta ‘Operation Hadin Kai’ da ke karkashin bataliya ta 195 suka gudanar, tare da hadin gwiwar rundunar sa kai ta farin kaya da aka fi sani da ‘Civilian JTF’.

Sanarwar ta ce dakarun sun kuma sami nasarar karbe wasu kayayyaki da ake kudurin kai wa ‘yan ta’adda a wannan samamen.

Ta kara da cewar kayayyakin da aka kwace sun hada da mota daya, kekune biyar, wayoyin salula biyu, man fetur da bakin mai, bindigar harba gurneti da kuma adda.

Haka kuma an sami karbe magunguna da suka hada da kara karfin maza, maganin kwari, kayayyakin abinci da sauransu.

Karin bayani akan: Brig. Gen. Onyema Nwachukwu, Manjo Janar Faruk Yahaya, Civilian JTF, sojin, Operation Hadin Kai, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.

Wasu makamai da dakarun Najeriya suka kwato a hannun mayakan Boko Haram a Geidam (Twitter/@H2NigerianArmy)
Wasu makamai da dakarun Najeriya suka kwato a hannun mayakan Boko Haram a Geidam (Twitter/@H2NigerianArmy)

Sanarwar ta ce dakarun sun kuma karade yankin baki daya, suka kuma tarwatsa dukan sansanonin da aka gano na ‘yan ta’adda ne.

"Babban hafsan soji Manjo Janar Faruk Yahaya ya jinjinawa kokarin sojojin, kana kuma ya yi kira garesu da su dore da aikin na su na matsantawa, domin ganin sun ‘yantar da dukan yankunan da ‘yan ta’adda suka mamaye” in ji sanarwar.

XS
SM
MD
LG