Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kara Cafke Wasu 'Yan Boko Haram


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sulalo cikin birnin Maiduguri da bamabamai guda ashirin da suka shirya domin su tadasu a wurare daban daban cikin birnin,

Kanar Tukur Gusau jami'in hulda da manema labarai na rundunar sojin najeriya dake fafatawa da 'yan Boko Haram a arewa maso gabas ya zanta da Muryar Amurka akan nasarorin da suke samu.

Kanar Tukur Gusau yace sojojin dake kula da Maiduguri sun samu nasarar cafke wani da ake kira John Trankil a anguwar kasuwar shanu. John ya fada masu cewa su tara suka shiga garin Maiduguri kowanensu dauke da bindiga kana suna da bamabamai guda ashirin.

Inji Kanar Gusau sun bada sanarwar kamanin motar kirar hilux fara da a nemeta a kuma sanarda jami'an tsaro saboda a kamasu.

A gefen Bama kuma sojojin sun gano inda 'yan ta'adan ke kera makaman kunar bakin wake da kuma rokoki. Sojojin sun samu kaya da dama a wurin. Sojojin na zaton 'yan ta'adan sun sato wasu daga cikin kayan ne daga wasu makarantun kimiya da suka kwace da can. Sojoji sun lalata kayan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG