Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Saki Firai Ministan Sudan Abdallah Hamdok Da Mai Dakinsa


Abdalla Hamdok

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaba da sakin Hamdok inda ya ce har sun gana da shi.

Dakarun da suka yi juyin mulki a Sudan sun saki Firai Ministan kasar Abdallah Hamdok tare da matarsa.

A ranar Litinin sojojin suka tsare Hamdok inda suka rusa majalisar da ke jagorantar gwamnatin hadakar kasar, suka kuma ayyana dokar ta-baci.

Jagoran juyin mulkin Janar Abdel Fattah al –Burhan ya ce sun kawar da gwamnatin hadakar mai dauke da sojoji da fararen hula ne saboda suna kokarin jefa kasar cikin matsalar tsaro.

Wata sanarwa da ofishin Hamdok ya fitar ta ce a daren ranar Talata aka sake shi da iyalinsa, “amma ana ci gaba da sa ido akansa.”

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaba da sakin Hamdok inda ya ce har sun gana da shi.

Blinken ya kuma yi kira ga sojojin da suka yi juyin mulkin da su saki dukkan shugabannin fararen hula da suke tsare da su.

Duk da wannan hatsinaya ta siyasa, jama’a da dama sun bazama akan titunan birnin Khartoun a ranar Talata don nuna adawarsu da juyin mulkin.

Wani kwamitin likitocin kasar ya ce akalla mutum hudu sun rasa rayukansu sannan an jikkata wasu 80 a ranar Litinin bayan da jami’an tsaro suka bude wuta akan masu zanga-zangar.

Janar Burhan ya tabbatar da tsare wasu ministoci da ‘yan siyasa inda ya ce wasu daga cikinsu za su fuskanci kuliya saboda rawar da suka taka wajen harzuka jama’a su yi bore ga dakarun kasar.

XS
SM
MD
LG