Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Shammaci ‘Yan Boko Haram


Wasu sojoji masu yaki da Boko Haram
Wasu sojoji masu yaki da Boko Haram

A wani sabon salo na yaki ba kungiyar Boko Haram, sojojin Najeriya sun shammace su, inda su ka yi masu barin wuta a wuraren boyewarsa da dama a arewa maso gabashin kasar.

Wannan jerin farmakin da aka kai ma ‘yan bindigar, ya faru ne a daidai lokacin da su kuma ‘yan ta’addan su ke kokarin dannawa garin Gamboru Ngala cikin motoci dauke da muggan bindigogi, amma su ka yi rashin sa’a, sojojin Najeriya su ka masu kaca kaca.

Haka zalika, sojojin Najeriya sun kai farmaki ma ‘yan Boko Haram din a wasu sassa da dama – wani lokacin ma har da hadin gwiwar sojojin kasar waje. Rahoton da rundunar sojin Najeriya ta fitar na nuwa cewa an kashe ‘yan Boko Haram da dama a hare-haren na bazata.

Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG