Ministan harkokin tsaron kasar Afghanistan yace a kalla sojoji arba’in da hudu sun mutu a wani hari da mayakan Taliban suka kaiwa sansanin sojin kasar dake kudanci yau alhamis.
Sojoji tara suka ji rauni a harin da aka kai yau da asuba a sansanin dake Kandahar , yayinda wadansu shida suka bace. Ma’aikatar tace an kashe maharan Taliban goma.
A sanarwar da kungiyar Taliban ta bayar da ta dauki alhakin harin, tace sojoji sittin aka kashe.
Sun fara aukawa sansanin ne tare da kai harin kunar bakin wake a wata mota daga nan wani gungun mayaka ya kutsa sansanin suna ci gaba da bude wuta.
Wannan ne hari na uku mafi muni da kungiyar Taliban ta kaiwa cibiyoyin tsaro wannan makon, dukansu kuma da salo daya. A kalla mutane hamsin da biyu aka kashe a harin da aka kai wata cibiyar horarda ‘yan sanda dake birnin Gardez ranar Talata, aka kuma sake kai wani harin ranar a lardin Ghazni dake kudanci.
Facebook Forum