Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Horas Da Sojojin kasashen Yankin Tafkin Chadi.


Sojojin Amurka da Nijar sun kulla yarjejeniya
Sojojin Amurka da Nijar sun kulla yarjejeniya

Sojojin Saman Amurka sun horas da sojojin dake cikin yankin tafikin Chadi domin samun karin kwarewa ga ayyukan tsaro da kuma bada agajin gaggawa

Wannan horon da sojoji Amurka dake Turai suka baiwa sojojin saman Najeriya, Niger da Chadi dama Jamhuriyar Benin nada zummar zaburar da sojojin kasashen bisa harkokin tsaro da kuma aikin jin kai duk a lokaci guda.

Manjo Janar David Belderwin shine ke jagorantar sojojin na Amurka.

Yace ko baya ga horas da dakarun wadannan kasashen akan bada ayyukan kare kasa da ayyukan gaggawa haka kuma zai kara dankon zumunta tsakanin kasashen dake cikin wannan horaswan.

Shiko tsohon hafsan sojan Najeriya Air Kwamanda Baba Gamawa yace idan akayi la’akari da kwarewa ta dakarun na Amurka yace ba shakka wannan horon zai agaza gaya.

Tsohon hafsan yace ko ba kome sojojin na Amurka suna da wadatattun kayan aiki, kuma suna da kwarewa akan wannan lamari na tsaro musammam idan ka duba shekarun da suka kwashe suna wannan abu musammam ma a kasashen da suke zuwa inda ake yaki da sauran su.

Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayan 2’25

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG