Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Sake Gano Wasu Gawarwakin Sojoji Hudu


Dakarun Amurka sun gano karin gawarwakin wasu sojoji hudu da motarsu ta kife da su a lokacin ambaliyar ruwa da ta mamaye wani sasanin soji da ke Fort Hood a Texas.Hakan na nufin ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki mutane tara ke nan.

A yau Asabar Sakataren tsaron Amurka, Ash Carter, ya tabbatar da mutuwar sojoji tara a sansanin na Fort Hood.

A ranar Alhamis aka gano wasu gawarwaki biyar bayan da wata gingimarin motar sojojin ta kife a ambaliyar ruwa da ta mamaye sansanin.

Akalla sojoji uku ne suka tsira da rayukansu kuma suna cikin yanayi mai kyau a cewar rahotanni. Su dai dakarun suna halartar wani horo ne a sansanin a lokacin da ambaliyar ruwan ta abkawa sansasnin.

A cewar Carter, dakarun Amurka za su koyi darasi daga wannan ala’mari domin kaucewa aukuwar irin wannan hadari a nan gaba.

Yankin na Fort Hood, da ke da tafiyar kilomita 320 daga birnin Houston, ya sha fama da saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a ‘yan kwanakin da suka gabata.

XS
SM
MD
LG