Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Faransa Sun Kashe Mayakan Sa Kai 20 a Mali


Dakarun Faransa a kasar Mali.

Jiya Lahadi sojojin Faransa sun ce sun kashe mayakan sakai wajen 20 a kasar Mali, daura da kan iyakar kasar da Burkina Faso.

Jami'an sojin Faransa da kuma shaidu sun ce an kai harin ne ta sama da ta kasa a wani kurmin da ke yankin na Sahel.

Sojojin Faransa wajen 3,500 ne ke baje a fadin kasar ta Mali da Burkina Faso da da Chadi da Mauritania da Nijar su na fafatawa da masu tsattsauran ra'ayin addini.

Mali ta tsawaita dokar ta bacin da ta kafa da karin wasu watannin 6, a yayin da ta ke kokarin taka burki na wata kungiyar 'yan tawaye mai alaka da al-Qaida da ke arewacin kasar, da kuma wasu masu tsattsauran ra'ayin wadanda ke kaddamar da hare-hare daga Burkina Faso.

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG