Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Koyi Darasi Daga Tarzomar Da Suka Faru A Baya In Ji Paparoma


Paparoma da Limamin Masallaci Al Azhar

Paparoma Francis shugaban darikar Katolika ya kamalla ziyarar daya kai kasar Masar

Jiya Juma’a Paparoma Francis, ya gana da babban limamin Masalaci jam’iar Al Azhar a wajen wani taron Musulmi da Kirista kafin ya ziyarci shugaban yan darikar Coptic Orthodox Paparoma Tawadiros domin yi mishi ta’aziyar wadanda aka kashe a hare haren da aka kai coci coci a biranen Alexandria da kuma Tanta, a farkon wannan watan.

Paparoma Francis ya fadawa shugabanin Musulmi da Kirista a wajen taron na jiya Juma’a wanda shima kansa shugaban kasar Masar Abdel Fatah El Sissi ya halarta cewa ya kamata a koyi darasi daga tarzomar da suka faru a baya. Domin a cewar sa tarzoma da rigingimu babu abinda suke haifarwa illa masifa da kuma yin dana sani.

An dauki tsauraran matakan tsaro sosai akan Paparoman, amma ya isa filin wasani cikin yar karamar motarsa samfurin Fiat taga a bude.

Yayi abinda ya saba yi, ya zagaye filin wasanin cikin budadiyar mota samfurin Golf.

Fadar Paparoma ta ki ya soke ziyarar bayan an kai hare haren, haka kuma ta yi watsi da tayin ta aka yi masa na yin amfani da motar da harsashi baya huda ta.

Daya daga cikin burin ziyarar Paparoma a kasar Masar shine ganin an karfafa fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista a kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG