Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin India Sun Kashe Mutane 18 A Yankin Kashmir


Firayim Ministan India Manmohan Singh

A wani yaki da ta'addanci da sojojin India suka kaddamar a wurare uku a yankin Kashmir mutane 18 suka rasa rayukansu

An kashe mutane 18 a cikin wasu tashe tashen hankula a wurare dabam daban uku a jiya Lahadi, yayin da sojojin India suka gudanar da wani matakin yaki da ta’addanci a yankin Kashmir na kasar Indiya.


Babban darektan yan sandan yankin S.P. Vaid, yace mayakan sa kai 11 da sojoji uku da fararen hula guda hudu ne suka mutu a arangamar.


Yace mayakan sa kan da suka mutu a wannan rikici, yan wata kungiya ce da ake kira Hizbul Mujahideen, da kuma Lashkar-e-Tayaba wato (dakarun ma'bota hanyar gaskiya.). Amurka da India sun ayyana kungiyoyin biyu a matsayin yan ta’adda.


Vaid ya shaidawa Muryar Amurka cewa yayin wani shirin farauta da yan sanda ke yi, wani dan bindiga ya mika kansa ga yan sandan. Vaid ya ce matakin ya sami gagarumar nasara a cikin yan makwanni nan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG