Kwamandojin soja sun ce a bayan da aka shafe tsawon dare sojojin kawancen da Amurka ke jagoranci suna yin luguden wuta ta sama, da asuba kuma sai sojojin Iraqi suka kaddamar da farmaki kan wadannan unguwanni masu tarihi a cikin ganuwar Mosul, birni na biyu wajen girma a Iraqi.
Wadannan unguwanni dake cikin ganuwar Mosul sune kadai suka rage a hannun mayakan Daesh, wadanda suka kama birnin shekaru 3 da suka shige.
Akwai fararen hula dubu 100 da suka rage cikin wadannan unguwanni, inda suke cikin hali na ukubar rashin wadataccen abinci da magunguna, ga kuma hatsarin ana iya rutsawa da su a fadan da ake yi.
Tun a ranar 17 ga watan Oktobar shekarar da ta shige ne sojojin Iraqi suka kaddamar da farmakin kwato Mosul daga hannun mayakan Daesh. An samu nasarar fatattakar tsageran cikin sauri daga unguwannin dake gabashin birnin, amma kuma kwato bangaren yammacin birnin, wanda ya fi yawan jama’a kuma ya hada har da unguwannin da suke cikin ganuwa, yana daukar lokaci fiye da yadda aka yi tsammani.
Facebook Forum