Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kashe Wani Ba-Falasdine A Hebron.


Jami'an tsaron Isra'ila suka killace inda aka kaiwa sojanta hari a Hebron.

Wannan lamari ya auku ne a yankin Hebron inda ake zargin Ba-Falasdinen ya dabawa sojan Isra'ila wuka.

Sojojin Isra'ila tace dakarunta sun harbe suka kashe wani mutujm ba Falasdine wanda ya dabawa wani sojan kasar wuka a yammacin kogin Jordan.

Tarzoma r wacce ta auku a safiyar yau Asabar,lamarin ya faru ne a wani wurin tsaro a birnin Hebron dake rarrabe tsakanin Falasdinawa da yahudawa.

Wannan kuwa yana faruwa ne kwana daya bayan da sojojin na Isra'ila suka harbe suka kashe falasdinawa uku, da suka kai hari a wasu lamura na daban, a garin na Hebron da kuma gabashin birnin kudus.

Fiyeda falasdinawa metan da yahudawa 34 ne aka kashe a karin tarozma a yankin cikin shekara daya data shige.

Isra'ila tana aza laifin karin tashe tashen hankulan kan zugar a shugabannin a bnagaren siyasa da addini na Falasdinaw a suke yi.

Amma Falasdinawa suka ce tashe tashen hankula sakamakon bacin rai ne na mamaye na shekara da shekaru da Isra'ila take yi musu.

XS
SM
MD
LG