Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Israila Za Su Yi Anfani Da Harsashi Kan Masu Gangami A Zirin Gaza Muddin Akwai Barazanar Tsaro


 Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Israila
Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Israila

Kasar Israila ta sha alwashin yin anfani da harsashi akan masu shirin yin gangami a Zirin Gaza gobe Juma'a muddin aka yiwa tsaronta barazana

Sojojin Israila zasu yi anfani da harsashi na kwarai domin tarwatsa duk wani ganganmi da aka shirya yi gobe Jumaa a Zirin Gaza kamar yadda wani babban hafsan sojin Israila ya fada.

Isra'ila ta girke gwanayen harbi fiyeda 100 akan iyakar Zirin Gaza, kuma an baiwa sojoji izinin su bude wuta akan masu zanga zanga "muddin akwai barazana kan harkar tsaron Isra'ila", wani babban hafsan mayakan Isra'ila ya fadawa wata jaridar kasar jiya Laraba.

Masu shirya wannan gangamin suka ce suna sa ran dubban jama’a ne zasu amsa kiran ciki ko harda daukacin iyalan wasu mutane da zasu bayyana a wasu sansanoni biyar dake kan bakin iyaka a gobe Juma’a.

Gangamin wanda zai dauki tsawon sati 6, an shirya shi da zummar neman a kyale yan gudun hijira Falesdinawa su koma muhallansu na asali wanda yanzu yake Israila.

Ahalinda ake ciki kuma, masana suna bayyana fargabar karshenta za'a yi karon batta tsakanin Isra'ila da Iran kasashe mafiya karfin soja a gabas ta tsakiya, wadda idan ba'a yi hankali ba, rikicin zai jefa Amurka ciki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG