Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kasar Iraqi Sunyi Nasarar Kwace Birnin Hawija


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Sojojin Iraqi sun yi nasarar kwato birnin Hawija da yake hannun 'yan kungiyar IS,Ministan kasar Haider Al-Abadi yace wannan nasrar bata kasar Iraqi bane kawwai na duniya ne baki daya.

Sojojin Iraqi sun samu nasarar kame garin Hawija wanda ke karkashin yan yakin sa kan IS, kamar yadda Prime Ministan kasar Haider Al-Abadi ya bada sanarwa.

Haider Al-Abadi ya bayyana wannan nasarar ce a taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron a Paris. Al-Abadi ya kira wannan nasarar cewa ba ta kasar Iraqi ce ce kawai ba a’a ta duniya ce baki daya.

Sojojin Amurka dake marawa sojojin Iraqi baya tare da hadin gwiwar sojojin lema ta na ‘yan Shi’iya dake samun goyon baya Iran suna cikin sahun wadanda suka taka rawar gani a wannan yakin kwato Hawijan wanda aka fara a ranar 21 ga watan satunba.

Yanzu haka dai Sojojin na Iraqi sun samu nasarasr kwace kusan dukkan wuraren dake hannun IS din ciki ko har da Mosul birni na biyu mafi girma a kasar wanda aka kwato shi a cikin watan yuni.

Sai dai kawo yanzu ba wani cikakken bayani game da makomar fararen hula a wannan birni daya fada hannun sojojin na Iraqi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG