Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji A Pulka Sun Samo Wata Daga Cikin Daliban Chibok Da Aka Sace


Salomi Pugo, dalibar Chibok da sojoji suka kubutar alhamis 4 Janairu 2018

Sojojin Najeriya dake aiki karkashin shirin nan na Operation Lafiya Dole na yaki da 'yan Boko Haram, wadanda kuma suke da sansani a garin Pulka, sun ceto wata dalibar Chibok daga cikin wadanda aka sace a shekarar 2014.

Rundunar sojoijin Najeriya ta fada a shafinta na Twitter cewa binciken farko ya nuna cewa ita wannan daliba sunanta Salomi Pagu, kuma ita ce hotonta yake lamba ta 86 a cikin jerin hotunan daliban Chibok da aka fitar a bayan da aka sace su.

Rundunar ta ce an samu Salomi Pagu tare da wata karamar yarinya 'yar shekara 14 mai suna Jamila Adams.

A yanzu haka dai, dukkansu su na hannun sojoji, inda ake duba lafiyarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG